Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Kamfanonin bin diddigin Bloomberg da tashoshin jiragen ruwa sun ba da rahoton cewa: "Duk da iƙirarin da Centcom ta yi na cewa za a dakatar da zirga-zirgar jiragen ruwa gaba ɗaya a cikin sa'o'i 48 na farko na kawanyar amma rahoton bayanan tauraron dan adam ya nuna karya zoben kawanyar a tsakiyar Tekun Farisa." Jiragen Tankunan mai da aka sanya wa takunkumi, J-Samer (mai ɗaukar iskar gas) da babban jirgin ruwa na "Hang Lu", sun isa ruwan Iran ta hanyar ketare tsibirin Lark da Qeshm.
A cewar "Tanker Tarkaz", jimillar manyan jiragen ruwa 4 sun yi nasarar tsallake kawanyar a daren da ya gabata. Wadannan tankokin jiragen ruwa sun shiga Iran yayin da suke ɗauke da loda ganga miliyan 4 na mai na dala miliyan 400; Manyan Jiragen tankunan mai da suka yi jigilar sama da ganga miliyan 60 na man Iran tun daga shekarar 2023 ne. Wani abin lura a cikin wannan kawanya shi ne zirga-zirgar wasu daga cikin wadannan jiragen ruwa, ciki har da jirgin ruwa da wani babban jigilar kaya dauke da kayayyaki na yau da kullun tare da alamar bibiya ta (AIS).
Matakin ya nuna rashin tasiri na barazanar da manyan jiragen ruwan Amurka ke yi kan layukan jigilar kayayyaki na Iran, kamar yadda Washington ta yi ikirarin toshe tashoshin jiragen ruwa na Iran gaba daya.
Your Comment